Wakilan kasashe sun fice daga taron Baku yayin jawabin Isra’ila

Yayin da Isaac Herzog ya fara jawabi a ranar Alhamis wakilan kasashe sama da 10, sun fice daga zauren taron na CICA a Baku babban

Wakilan kasashe da dama, sun fice daga zauren taron tsaro na Asiya a Baku a yayin da shugaban Isra’ila ya fara gabatar da jawabi.

Yayin da Isaac Herzog ya fara jawabi a ranar Alhamis wakilan kasashe sama da 10, sun fice daga zauren taron na CICA a Baku babban birnin kasar Azerbaijan.

Wannan bas hi ne karo na farko ba da akje fuskantar irin haka inda ko a watan Satumba a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, wakilan kasashen da dama suka fice daga zauren yayin jawabin Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

Taron na yini guda da aka gudanar ranar Alhamis, wanda kasar Azerbaijan ta karbi bakuncinsa a matsayinta na mai jagorantar kungiyar ta CICA a halin yanzu, ya hada wakilan kasashe mambobi, kasashen da ke da matsayin masu sa ido, da kuma kungiyoyin kasa da kasa da ke hadin gwiwa da kungiyar.

Firaministan Turkiyya Hakan Fidan daya daga cikin kasashen da wakilansu suka fice daga zauren taron ya bayyana cewa ya kamata kasashe mambobin kungiyar CICA su dauki matsayi mai karfi wajen goyon bayan hakkokin Falasdinu da kuma nuna adawa da zaluncin da ake ci gaba da tafkawa da kuma mummunan take hakkin dan adam.

Tun daga watan Oktoban 2023, an kashe Falasdinawa sama da 74,000, yayin da wasu fiye da 175,000 suka jikkata a Gaza sakamakon kisan kare dangi da Isra’ila ke yi; kuma kusan kashi 90 cikin dari na kayayyakin more rayuwa a yankin sun lalace ko kuma an ruguza su gaba daya.

Haka kuma, hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, da kuma farmakin da yahudawan da suka mamaye yankunan Falasdinu ba bisa ka’ida ba ke kaiwa kan Falasdinawa da dukiyoyinsu, sun karu sosai a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ciki har da Gabashin Kudus tun daga wancan lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted