Rundunar sojin ruwa ta dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran IRGC ta bayyana cewa wasu tankokin mai fetur gud 3 sun kama da wuta a mashigar hormuz bayan da suka yi kokarin satar hanya wajen ganin sun wuce ta mashigar wanda hakan karta dokokin da kasar iran ta shimfida ne ga jirage masu wucewa
Acikin wani bayani da dakarun suka fitar a yau lahadi ya nuna cewa hatsarin ya faru ne da safiyar yau bayan da aka ga turnukewar hayaki daga wasu jiragen ruwa da suke konewa a kusa da mashigar hormuz sakakamon karya dokokin da suke yi na kokorin wucewa ba tare da sun nemi izini ba.
Wannan bayani yazo ne kasa da kwana daya da wasu tankokin mai din guda biyu suka kama da wuta bayan da suka ci karo da nakiya da dakarun kare juyin na iran suka dasa a mashigar Hurmuz domin hukunta duk wani jirgin ruwa da yayi kokarin shigewa ta mashigar ba tare da izini ba,
Iran ta dauki tsauraran matakai a mashigar hormuz ne domin mayar da martani game da hare haren da Amurka da isra’ila suka kai mata da ya fara a ranar 28 ga watan fabarerun shekara ta 2026 da muke ciki.