Wasu daga cikin kasashen Turai na ci gaba da bai wa Isra’ila makamai yayin da take ƙara kai munanan hare-hare a Zirin Gaza sannan kuma ana zarginta da aikata laifin kisan ƙare-dangi.
Kamfanin dillacin labarai na Turkiyya Anadolu ya tattara wasu muhimman bayanai kan yadda kasashen Turai ke sayar wa Isra’ila makamai tun daga fara yaƙin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba na 2023.
A tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023 ƙasashen Faransa da Italiya da Jamus da kuma Amurka suna da kaso 81 cikin 100 na makaman da ake shigarwa yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar cibiyar nazari da bincike kan rikice-rikice da zaman lafiya a duniya Stockholm (SIPRI) da ke ƙasar Sweden.
Kudaden da Isra’ila ke kashewa na makamai ya ƙaru da kashi 24 cikin 100 zuwa dala biliyan 27.5 bayan hare-haren da ta kai a Gaza, lamarin da ya sa ta kasance ƙasa ta biyu a yawan kashe kudi kan makamai a Gabas ta Tsakiya.
Daga shekarar 2014 zuwa 2022, Ƙungiyar Tarayyar Turai EU ta ba da lasisin fitar da makaman da suka kai na kimanin dala biliyan 6.8 (€ 6.3 biliyan) zuwa Isra’ila.
Ana dai zargin wadannan makamai da sanadin mutuwar fararen hula fiye da 38,000 a Gaza, wadanda suka hada da mata 10,000 da ƙananan yara fiye da 15,000.
Ko da yake wasu kasashen Turai da suka hada da Belgium da Italiya da Netherlands da Sifaniya sun yanke shawarar dakatar da sayar da makamai ga Isra’ila, sai dai wasu rahotanni sun yi zargi cewa har yanzu akwai alamun ana ci gaba da cinikin makaman.