Washington Post: Cikin Wasu Kasashen Larabawa Ya Duri Ruwa kan  Binciken Trump

Washington Post ta bayyana cewa gwamnatocin Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Qatar hantarsu ta kada kan batun shirin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci

kasashen larabawa da Trump

Washington Post ta bayyana cewa gwamnatocin Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Qatar hantarsu ta kada kan batun shirin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ke da alaƙa da Shugaban Amurka Donald Trump, gwamnatinsa, da iyalansa, bayan nasarar da ‘yan Democrat suka samu a zaɓen ‘yan majalisa.

Jaridar ta ambato jami’ai a Washington da Gulf suna cewa ‘yan majalisar Democrat sun yi wa ƙasashen uku gargaɗi game da binciken da ake sa ran yi, wanda ake sa ran zai haɗa da yarjejeniyar gidaje, saka hannun jari a harkokin kuɗi, da kyaututtuka da suka shafi Trump da abokan aikinsa.

‘Yan majalisar sun kuma yi gargaɗin cewa rashin haɗin kai da binciken zai iya kawo cikas ga dangantakar waɗannan ƙasashe da Amurka. A halin yanzu, jami’an diflomasiyya da majiyoyi masu tushe suna shakkun cewa gwamnatocin Gulf za su samar da bayanai masu mahimmanci, gami da wasiƙun sirri, waɗanda masu bincike za su iya buƙata.

Jaridar ta lura cewa waɗannan abubuwan sun faru ne yayin da yaƙin da Iran ya shiga watan tara, wanda ya yi daidai da Ma’aikatar Tsaron Amurka tana sake duba girman kasancewar sojojinta a yankin bayan watanni da hare-haren Iran a sansanonin Amurka.

A cewar jaridar The Washington Post, ana sa ran za a yi bincike sosai kan hannun jarin Daular Larabawa na dala miliyan 500 a cikin World Liberty Financial, wani kamfanin cryptocurrency da ke da alaƙa da iyalan Trump.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted