Tsohon magajin garin Bacelona Ada collaou da sauran masu rajin kare hakkin dan adam yan kasar spaniya dake cikin jiragen ruwan agaji na Sumud Flotilla da Isra’ila ta kama a baya bayan nan, sun yi tir da irin azabartar da su da isra’ila ta yi kuma sun sha alwashin daukar matakin shari’a a kanta,
Shi ma shugaban bangaren hagu na jam’iyar podemos ya sanar da shirye shiryen maka prime minister Isra’ila Benjamen na tanyaho a gaban kuliya manta sabo,
Matakin shariya da kungiyoyinn farar hula da sauran jam’iyun siyasa a kasar Spaina ta dauka yana kara nuna yadda duniya ke yin matsin lamba kan gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma zai sanya bangaren sharia na kasar spain ya gudanar da bincike na musamman kan batun ,da kuma kotun ICC ya kara mayar da gwamnatin saniyar ware .
Wannan abin da ya faru wani bangare ne na gangami wajen ganin an karya killacewar da aka yi wa yankin Gaza ta hanyar aikewa da kayan agaji ta jirgin ruwa, wanda ke fuskantar mayar da martani daga sojojin HKI ,kuma ya nuna yadda yakin Gaza ke ci gaba da daukar hankali duniya kuma yayi tasiri a bangaren siyasa a kasashen turai kamar kasar Spain .