Wani Kamfanin Kera Kayan Aikin Likitanci Ya Gabatar Da Sabuwar Na’urar Tiyata

Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa

Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda ke gudana a nan birnin Tehran.

Labarin ya kara da cewa samar da kayalin aikin likita wadanda suke tafiya da zamani, ya zama dole ne bayanda aka haka sayarwa kasar Iran irinsu daga waje.

Wannan hanin ya sa a dole daga cikin gida kwararru suka fara samar da kayakin aikin likita na zamani, don wadatar da asbitocin kasar daga sayan na waje, har ma tana sayarwa kasashen waje.

Mostafa Abdulgaffar shugaban kamfanin da ya samar da wannan na’urar yace : Na’urar za ta taimakawa lokitoci da wasu ayyuka masu muhimmanci dangane da marasa lafiyan da sukewa aiki, ta yadda likitocin ba za su yi kuskure na bata wani wuri a cikin jikin marasa lafiya wanda sukewa aiki ba.

Abdulgaffar ya kara da cewa kafin haka kasar Iran tana shigo da irin wadannan kayakin aikin likita ne daga kasashen Amurka, da Jamus. Amma bayan an dorawa kasar takunkuman tattalin arziki, sun dukufa a cikin gida saida suka samar da su. Suka kuma sami lasicin aiki da su a cikin asbitocin kasar da kuma saida su ga kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments