Wani Harin Saudiyya Ya Lalata Ginin Kamfanin Mai Na Yemen

Kafafen yada labaran ba su bayar da wani cikakken bayani game da asarar rayuka ko kuma irin barnar da harin ya yi ba.

Bayanai daga Yemen na cewa wani gini mallakar Kamfanin Mai da Iskar Gas na Yemen (YOGC), ya lalace bayan fuskantar hare-haren jiragen saman Saudiyya a Sanaa.

A cewar tashar talabijin ta Yemen Al Masirah, wadda ta ambato majiyoyin yankin, jiragen saman Saudiyya sun kai hari kan ginin da ke kan titin al-Sittin da ke gundumar al-Wahda da safiyar Talata.

Kafafen yada labaran ba su bayar da wani cikakken bayani game da asarar rayuka ko kuma irin barnar da harin ya yi ba.

Jiragen saman Saudiyya sun kuma kai hari kan tashar mai ta al-Mufzar, wacce ke yankin Jader na gundumar Bani al-Harith.

Wadannan sabbin hare-haren sun zo ne ‘yan sa’o’i bayan da mai magana da yawun rundunar sojin Yemen ya sanar da cewa rundunonin tsaron sama na kasar sun gano kuma sun harbo wani jirgin leken asiri na CH-4 na rundunar sojin saman Saudiyya da aka kera a China.

Sabon tashin hankali a Yemen ya samo asali ne sakamakon harin bam da rundunar sojin saman Saudiyya ta kai a filin jirgin saman kasa da kasa na Sana’a a watan Yuli.

A matsayin martani, sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filayen jiragen saman Saudiyya, wuraren mai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted