Ma’aikatar lafiya ta kasar Labanon ta ce hare-haren da Isra’ila ta kai kan kauyukan da ke kudancin kasar ya yi sanadin mutuwar likitoci akalla biyu.
Ma’aikatar ta fada a yau Asabar cewa, farmakin da Isra’ilan ta kai kan wata tawagar bayar da agajin gaggawa a garin Kfar Tebnit da ke kudancin kasar, ya yi sanadin mutuwar wani likita guda tare da jikkata wasu hudu yayin da wasu likitoci biyu suka bace.
A ci gaba da cewa an kuma kashe wani ma’aikacin jinya a wani harin da Isra’ila ta kai a garin Borj Rahal da ke gundumar Tire a kudancin Lebanon.
A halin da ake ciki kuma jiragen yakin Isra’ila sun kai wani mummunan hari a unguwar Haret Hreik da ke kudancin birnin Beirut na kasar Labanon.
A karshen watan Satumba ne Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa da kuma wani gagarumin farmaki ta sama kan kasar Lebanon bayan shafe shekara guda tana musayar wuta a kan iyakar Lebanon a daidai lokacin da yakin Gaza.
Akalla mutane 3,287 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Lebanon cikin shekara guda, wanda akasarin mafi yawa a cikin makonni bakwai da suka gabata.
Wasu 14,222 kuma sun sami raunuka, galibi mata da yara.