Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa

Wani babban dan majalisar dokokin kasar Iran ya ja kunnen kasar Amurka kan taba jiragen ruwan dakon danyen man kasar Iran a tekun farisa ko

Wani babban dan majalisar dokokin kasar Iran ya ja kunnen kasar Amurka kan taba jiragen ruwan dakon danyen man kasar Iran a tekun farisa ko a wani wuri.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Alaeddon Burujardi dan majalisar dokokin kasar Iran sannan mamba a kwamitin al-amuran kasashen waje da kuma tsaron kasa yana fadar haka.

Ya kuma kara da cewa duk wanda ya taba jiragen ruwan daukan man fetur na Iran wadanda suke dauke da danyen man fetur zuwa kasashen waje, ya san cewa iran ba zata kyale ba. Burujaedi ya bayyana cewa Washington ta san karfin sojojin ruwa na kasar Iran a bayan. Ya ce idan Amurka ta kuskura ta taba jirgin ruwan dakon mai na kasar Iran ta san cewa zata rama maida martani masu tsanani. Burujardi ya bayyana haka ne bayanda gwamnatin Amurka ta dorawa wasu mutane 50 da kuma kamfanonin jiragen ruwa masu jigilar danyen man fetur na kasar Iran daga kasashen UAE, Hong Kong da kuma China,takunkuman tattalin arziki

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted