UNRWA : hana shigar da kayan agaji Gaza, ya jefa yankin cikin matsanancin hali

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci.

“Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza.

“Ba abinci, ba magani, ba ruwa, babu man fetur,” inji Philippe Lazzarini a cikin wani sako a shafukan sada zumunta.

Tun a ranar 4 ga watan Maris ne Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, bayan karewar kashi na farko na tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar gwagwarmayar falasdianwa ta Hamas data kunshi musayar fursunoni tsakanin bangarorin.

Lazzarini ya jaddada cewa al’ummar Gaza sun dogara ne kan shigo da kayayyaki daga yankunan da aka mamaye.

“Duk ranar da ta wuce ba tare da agajin jin kai ba, hakan na nufin yara da yawa suna kwana da yunwa, cututtuka na yaduwa,” in ji babban jami’in UNRWA.

Lazzarini ya bayyana haramcin taimakon a matsayin wani hukuncin bai daya ga al’ummar Gaza, wadanda akasarinsu kananan yara ne da mata.

Ya yi kira da a dage wannan kawanya da kuma kai agajin jin kai da kayayyakin kasuwanci zuwa Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments