A jiya Asabar ce kasashen Rasha da Ukraine suka yi musayar Fursinoni a tsakanin, karon farko irinsa tun bayan fara yaki a tsakaninsu fiye da shekaru 3 da suka gabata.
Shafin yanar gizo na Labarai Arabs News ya bayyana cewa an yi musayar furisnonin ne a jiya Asabar kuma ko wace kasa ta sake fursinonin yaki har 390.
Labarin ya kara da cewa a dai dai lokacinda aka yi musayar fursinonin sojojin Rasha sun yi loguden wuta a kan birnin Kiyev babban birnin kasar ta Ukraine.
Majiyar gwamnatin kasar Ukraine ta bada sanarwan cewa akalla mutane 10 sun ji rauni saboda luguden watan.
A makon da ya gabata ne kasashen biyu suka tattauna a tsakaninsu a birnin Istambul na kasar Turkiyya, inda ake saran zasu tsagaita budewa juna wuta amma hakan bai faru ba saboda sabanin da ke tsakanin kasashen biyu. Amma duk da haka sun amince su yi musayar fursinoni a tsakaninsu wanda ya tabbata a jiya. Ana saran kasashen biyu zasu sake haduwa nan kusa a kokarin tsagaita wuta a tsakaninsu.