Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky yayi suka mai tsanani ga magoya bayansa , kuma ya zargesu da samar da makamai kadan da ba zasu wadatar ba ga gwamnatin Kiev, kuma ya sanya alamar tambaya ga aikin da gamayyar kasa da kasa dake nuna goyon bayan su ke yi adaidai lokacin da ake fuskantar jinkiri wajen isar musu da makamai
A cikin sakon bidiyo da ya aike da shi yace yanzu muna kokarin gudanar da bincike game da ayyukan gamayyar da suke nuna goyon bayansu ga ukrain ne, don gane wanda ke aiki da nauyinsa daga cikinsu da kuma wanda suke yi da gaske ba alkawarin karya ba , zamu yi kokari wajen tantance wadannan abubuwan.
Ko da yake har yanzu abubuwa basu kasance afili ba, inda ba’a san inda wadanda ke nuna goyon bayan zelensky suka fuskanta ba, adaidai lokacin da batun tattaunawar sulhu tsakanin ukraine da Rasha babu wani tabbaci a kai , wanda yanayin ya sanya shakku tsakanini alummar duniya
Ana sa bangaren shugaban kasar faransa Emanuel macron ya wallafa wani bayani a shafinsa na x inda ya soki yanayin karaya da ke kudundune da tattaunawar zaman lafiyar Ukrain, yace amincewa da yarjejeniyar zaman lafiyar ta rashin adalci da kasar rasha zai cutar da tsaron kasashen turai .