Turkiyya Ta Yi Gargadi Akan Sake Kai Hari Kan Iran

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi gargadin cewa wani sabon hari kan Iran zai kara yaɗa yaƙi da rikici a yankin.

Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya Hakan Fidan ya ce daukar mataki na soja kan Iran ba mafita ba ce ko kaɗan, bayan taron R4+E3 a Istanbul.

Ya bayyana hakan ne a taron Istanbul da Masar, Pakistan da Saudiyya, domin fifita wasu matakai na diflomasiyya maimaikan amfani da karfi.

Kasashen hudu sun kafa tsarin R4 da zummar karfafa hadin gwiwa kan batutuwan yankin.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi gargadin cewa wani sabon hari kan Iran zai kara yaɗa yaƙi da rikici a yankin yayin da tashin hankali tsakanin Washington da Tehran ke ƙara ta’azzara.

“Shiga tsakani na soja a Iran ba mafita ba ce ko kaɗan. Babu wanda ke goyon bayan wannan a yanzu,” kamar Hakan Fidan ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a bayan taron R4+E3 a Istanbul, taron farko da aka taɓa yi a wannan tsari.

Wanann dai an zuwa ne a daidai lokacin da ake cewa Amurka da Isra’ila sun tsara shirye-shiryen sake kai hare-hare kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adi na Amurka.

Türkiye, Masar, Pakistan da Saudiyya ne suka kafa tsarin R4 don tallafawa zaman lafiya mai ɗorewa da kuma ƙarfafa tattaunawa kan batutuwan yankin.

Ministocin harkokin waje na R4 sun gudanar da taruka shida zuwa yanzu, inda aka fara gudanar da taron farko a Riyadh a ranar 18 ga Maris.

Taron da aka yi kwanan nan a wannan tsari an gudanar da shi ne a birnin New York a ranar 21 ga Satumba a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Tsarin E3, wanda ya kunshi Jamus, Birtaniya da Faransa, an kafa shi ne a shekarar 2003 a matsayin wani bangare na hadin gwiwar diflomasiyya tsakanin kasashen uku game da shirin nukiliya na Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted