Turkiyya Ta Bukaci Da A Kakabawa Isra’ila Takunkumai  

Turkiyya ta bukaci da a kakabawa Isra’ila takunkumi sakanakon yakin da take yi a Gaza da kuma hare-haren da take kai wa Lebanon. Ministan harkokin

Turkiyya ta bukaci da a kakabawa Isra’ila takunkumi sakanakon yakin da take yi a Gaza da kuma hare-haren da take kai wa Lebanon.

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya, Hakan Fidan ya yi kira ga kasashen duniya da su kakabawa Isra’ila takunkumi kan hare-haren da take kaiwa Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa kasar Labanon.

Turkiyya ta bayyana cewa lokacin diflomasiyya ya wuce, “dole ne mu kaurace wa Isra’ila”.

Dama dai Turkiyya ta yanke yawancin huldar tattalin arzikinta da Isra’ila.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki tsarin kasashen duniya da cewa an tsara shi ne don wasu zababbun kasashe ‘yan gata su ci gajiyarsa, inda ya buga misali da abubuwan da ke faruwa a Gaza.

“Abin da ke faruwa a Gaza hujja ce kwakkwara ta cewa an tsara tsarin kasa da kasa ta yadda ake amfani da shi wajen cin zarafin wasu ‘yan tsiraru,” in ji Fidan a ranar Talata yayin taron diflomasiyya kan makomar Falasdinu a Ankara.

Ya kuma bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin kisan kare dangi, yana mai cewa an kashe mutum 42,000 galibi mata da kananan yara, da ganganci da kuma tsari.

Ministan Harkokin Wajen na Turkiyya ya kuma nanata matsayin Turkiyya kan samar da kasashe biyu a matsayin hanya daya tilo da za ta samar da zaman lafiya, yana mai cewa, sama da kasashe 150 ne suka amince da Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments