Jonathan: Ya Damu Da Yanda Neman Zabe Ke Tafiya A Kasar

Tsohon shugaban  tarayyar Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya bayyana damuwarsa da yanda yakin neman zaben shugaban kasa da gwamnoni na shekara mai zuwa yake tafiya

Tsohon shugaban  tarayyar Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya bayyana damuwarsa da yanda yakin neman zaben shugaban kasa da gwamnoni na shekara mai zuwa yake tafiya a kasar, saboda akwai tashe tashen hankula da suka shafi kabilanci, yankuna da bangarinci ciki a cikinsu, wadanda kuma suna iya shafar zaman lafiya da hadin kan kasar nan gaba.

Jaridar Daily Trust ta najeriya ta nakalto tsohon shugaban kasar na fadar haka a jiya Talata ya kumakara da cewa, ana gudanar da yakin neman zaben tare da amfani da yan banga, ba wanda yake yarda da ra’ayin da ya sabawa ra’ayinsa. Ya kuma bayyana haka a cibiyar Goodluck Jonathan da ke Abuja, a kuma taro inda aka tattauna kan matsalolin tsaro da zaman lafiya a kasar.

Tsohon shugaban  ya ce har yanzun yana ci gaba da sabon sakonni daga yan uwa da abokan arziki daga ciki da wajen kasar wadanda suke nuna damuwarsu da yanda yakin neman zabe na shekara mai zuwa yake tafiya. Daga karshe ya bukaci yan Najeriya sun mutunta juna suamince da yanda ake zama a kasar tare da bambance bambance da ke tsakanimmu tun shekaru aroaro da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted