Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka
Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora wa Iran, ba wai kawai bai cimma komai ga Isra’ila ba ne, har ma ya canza daidaiton dabarun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila gaba ɗaya.
A lokacin taron tattaunawa na 31 na ƙungiyar Jaruman Musulunci a Qom, Hussein Ta’ib ya ce: “Dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Iran sun kalubalanci masu girman kai inda suka kai wani mataki cikin saurin na zarce lissafin siyasa da tsaro idan aka kimanta.”
Da yake magana game da bitar dabarun tsaron ƙasa na Amurka bayan rugujewar Tarayyar Soviet, Hussein Taeb ya ce: “Burin farko na Amurka da zarar an shiga shekara ta 2025 shine mayar da hankali kan kawar da duk wata cikas gare ta daga ikon duniya. Duk da haka, a cikin bitar shekara ta 2020, Amurkawa sun yarda cewa ba a cimma wannan burin ba kuma sun ayyana shekaru goma daga 2020 zuwa 2030 a matsayin shekaru goma masu mahimmanci ga makomarsu da makomar Gabas ta Tsakiya.”
Yakin Da Akayi Tsakanin Iran Da HKI Ya Canza Tunanin Duniya,Harma Da Tsorotorwa Ga Munafikan Duniya, Allah Yasa Iran Tayi Nasara Akan Duk Wani Munafiki.
mun gode