Rahotonni sun bayyana cewa: Hare-haren da tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida suke kai wa kan yankunan Falasdinawa daban-daban da suke Yammacin Gabar Kogin Jordan na karuwa sosai.
A wani sabon rikici da ya barke, sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan garin Ya`bad da ke kudu maso yammacin Jenin a shiyar arewacin gabar yammacin kogin Jordan, sakamakon arangama da sojojin mamayar suka yi da Falasdinawa, inda sojojin mamayar suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya kai ga shahadar Falasdinawa ciki har da yaro dan shekaru 13 a duniya.
A garin Ramallah a kauyen Al-Mughayyir da ke gabashin birnin, sojojin mamayar haramtacciyar kasar sun ci gaba da kai hare-hare tsawon kwanaki biyu, inda aka kara yawan sojojin mamaya da suke kai farmaki kan kauyen, lamarin da ya sa aka dakatar da tafiyar yara zuwa makaranta a kauyen. Sojojin mamayar sun kuma kai farmaki a garin Sa’ir da ke arewacin Khalil da kuma garin Tuqu’u da suke kudu maso gabashin birnin Beit-Laham, sakamakon haka arangama ta kunno kai tsakanin matasan Falasdinawa da sojojin mamayar tare da kama wani matashi dan garin baya ga wasu samari guda biyu a garin Sa’ir dake arewacin Khalil, yayin da sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Aroub da ke wannan yankin ya sha fama da hare-haren wuce gona da iri da kamen Falasdinawa.