Wani Bafalasdine ya yi shahada sakamakon harbin bindiga daga tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa ta sanar da shahadan wani matashi sakamakon raunukan da ya samu a harin da tsagerun yahudawan sahayoniyya suka kai a garin Mikhmas, arewa maso gabashin birnin Kudus da aka mamaye. A halin yanzu, Jordan ta yi kira da a dauki matakin kasa da kasa don dakatar da karuwar tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
An kashe Nasrallah Muhammad Jamal Abu Siam, mai shekaru 19, bayan da wasu hudu suka jikkata, uku daga cikinsu da harsasai masu rai, a lokacin harin da tsagerun yaahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida suka kai karkashin kariyar sojojin mamayar Isra’ila. Harin ya kunshi harbin bindiga da kuma sace tumakai da dama daga manoman Falasdinawa.
Kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta Falasdinawa ta bayar da rahoton cewa: Ma’aikatanta sun kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti, inda ta lura cewa: Daya daga cikinsu yana cikin mawuyacin hali kafin daga baya ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.