Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar Ukrain.
Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.