Fadar White House ta sanar cewa, shugabannin Kasashen Amurka, Sin, da kuma Rasha za su gudanar da wani taron bangarori uku na musamman a mako mai zuwa, a gefen taron kolin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik (APEC) da za a yi a birnin Shenzhen.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, wanda ya ambato wani babban jami’in Amurka, ya rawaito cewa Trump na shirin tattauna batun yaki da Iran tare da Xi da Putin.
Sai dai, kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya bayyana cewa duk wata yarjejeniya da za a iya cimmawa a Shenzhen ba za a iya tilasta wa wasu kasashe su bi ta ba.
Ya ce tsarin duniya ya kamata ya ginu ne bisa “amfanar juna da girmama juna,” maimakon kokarin tilasta wa wasu ra’ayi na musamman.
Yiwuwar gudanar da wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da Beijing da Moscow ke sukar Amurka kan yawan kai hare-hare a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da hadin gwiwar gwamnatin Isra’ila.
Wannan hare-hare ya sa Tehran ta rufe mashigar ruwa mai muhimmanci ta Mashigar Hormuz, a matsayin martani ga abokan gabanta da kawayensu, wadanda suka yi amfani da hanyar ruwan wajen kai hari kan kasar Iran ko kuma tilasta wucewar jiragen ruwa ta wannan mashiga ba bisa ka’ida ba.
Rufe mashigar ya haifar da rudani a kasuwannin makamashi na duniya, inda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya tilasta wa kasar Sin fitar da adadi mai yawa na man da ta ajiye a matsayin tanadi domin daidaita kasuwannin makamashi.