Shugaban Sin, Xi Jinping, ya yi ganawar farko da takwarorinsa na Rasha Vladimir Putin da Donald Trump na Amurka a jajibirin taronsu a birnin Shenzhen.
Xi Jinping ya gana da Shugabannin a wata liyafa a gefen taron hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya da Pacific (APEC).
Wannan kuma shi ne karo na farko da Donald Trump da Vladimir Putin suka gana tun bayan taronsu a Alaska a watan Agusta na 2025.
Tunda farko Shugaba Xi, ya tarbi takwarana na Rasha Vladimir Putin, inda ya yaba da ci gaban da aka samu a dangantakar kasashen biyu, sannan ya yi kira da a karfafa hadin gwiwarsu.
Ya yi kira ga dukkan kasashen biyu da su dauki nauyin da ke kansu na kasa da kasa gaba daya, sannan su bayar da gudummawa ga hada kan duniya da kuma kara huldar dimokuradiyya a huldar kasa da kasa.
A nasa bangaren, Vladimir Putin ya kare juriyar tattalin arzikin Rasha a gaban takunkumin kasashen yamma.
A cewarsa, takunkumi, haraji, da takunkumin fitar da kaya sun rasa tasirinsu sosai kuma ba za su iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin da aka yi niyya ba.
A nasa bangaren shugaban Amurka Donald Trump ya ambaci yiwuwar tattaunawa kan kawar da makaman nukiliya da rikice-rikicen da ke faruwa a Iran da Ukraine a lokacin taron da aka sanar da cewa zai yi da Xi Jinping da Vladimir Putin.