Tehran Ta Yi Kira Da A Fitar Da Isra’ila Daga Kungiyar CICA

Kazem Gharibabadi, ya bayyana matsayin Iran kan ci gaban yanki da na kasa da kasa, da kuma yanayin tsaro a Asiya.

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta yi kira da a fitar da Isra’ila daga zama mamba a kungiyar tsaro ta Asiya CICA.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya ayyana Isra’ila a matsayin “babban tushen rashin tsaro da rashin zaman lafiya a Asiya, musamman a Gabas ta Tsakiya.”

Yana kira ga kasashen mambobi da su daina shiru game da “laifukan zalunci” da ‘yan Sahayoniya ta aikata kan kasashe masu ‘yancin kai da dama  tare da goyon bayan Amurka inda ya yi ikirarin cewa lokaci ya yi da za a ware wannan gwamnatin daga kungiyar.

Kazem Gharibabadi, ya bayyana matsayin Iran kan ci gaban yanki da na kasa da kasa, da kuma yanayin tsaro a Asiya, a lokacin jawabinsa a taron koli kan Mu’amala da matakan gina Aminci a Asiya (CICA).

“Taron na bana na kungiyar na gudana ne a wani yanayi inda Asiya, duk da yawan dan adam din ta, tattalin arziki, da wayewa, ke fuskantar jerin barazanar tsaro masu sarkakiya,” in ji shi.

Ya yi kira ga ƙasashen da ke cikin ƙungiyar da kada su yi shiru game da abin da ya bayyana a matsayin “laifukan mugunta” da Isra’ila ta aikata a kan ƙasashe da dama, tare da goyon bayan “uwargidanta,” Amurka, yana mai ƙara da cewa yanzu lokaci ya yi da za a kori Isra’ila daga CICA.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan hadin gwiwa a yankin, hanyoyin sadarwa da zirga-zirga, amfani da fasahar dijital, da kuma ci gaba mai dorewa, a karkashin jagorancin Azerbaijan.

Ana sa ran taron zai amince da wata sanarwa da ake kira ‘Sanarwar Baku’ da kuma wata takarda kan hadin gwiwa a fannin lafiya da tsaro a wuraren aiki, tare da sanar da shigar kasar Laos a matsayin sabuwar mamba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted