Tawagogi Na Isa Lebanon Domin Halartar Jana’izar Sayyed Hassan Nasrallah

Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah. Iran, ma ta sanar da

Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah.

Iran, ma ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga zuwa kasar ta Lebanon domin halartar jana’izar shahiddan Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine.

A gobe Lahadi ne za a gudanar da jana’izar wadannan shahidai biyu a birnin Beirut, inda ake sa ran tawagogin daga kasashe 78 za su halarta.

Shugaban kwamitin da ke sa ido a jana’izar, Sheikh Ali Daher, ya sanar a ranar Juma’a cewa za a fara jana’izar a hukumance a ranar Lahadi daga karfe 1 na rana (agogon kasar).

Jami’ai da dama da suka hada da shugaban kasar Lebanon da kakakin majalisar dokokin kasar za su halarci jana’izar, ya kuma kara da cewa wata babbar tawaga ta Iran za ta halarci bikin ba tare da yin karin bayani ba.

Bugu da kari, Sheikh Naim Qassem babban sakataren kungiyar Hizbullah zai gabatar da jawabi a wajen bikin.

Idan dai ba a manta ba Sayyid Nasrallah ya yi shahada ne a wani harin bam na Isra’ila a kudancin birnin Beirut a ranar 27 ga watan Satumban 2024.

A nasa bangaren, Sayyed Safieddine ya yi shahada ne a wani harin da Isra’ila ta kai a watan Oktoban 2024.

Kungiyar Hizbullah ta zabi dage bikin jana’izar mutanen biyu, saboda hadarin halin da ake ciki na iya fuskantar hare-haren hare-haren Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments