Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai.
Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran kan cewa, babu hanyar da ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran sai hanyar Diblomasiyya.
Ya kumakara dacewa kungiyar tana maraba da duk wani ci gaba a wannan bangharen. Mai maganan ya kara da cewa wakilin EU a MDD ya yi wannan bayanin a gaban kwamitin tsaro na MDD a yan kwanakin da suka gabata.