Kungiyar Likitocin Sa-Kai ta ( Doctors Without Borders) ta bayyana cewa, mata da kananan yara suna mutuwa a yankin Darfur akan cutukan da za a iya magance su, saboda rashin magani da kayan aiki.
Rahoton da kungiyar ta fitar ya kunshi cewa; Daga watan Janairu na wannan shekara zuwa tsakiyar Ogusta, an sami mutuwar mata da kananan yara har sau 114.
Har ila yau, rahoton ya kuma ce, kaso 50% na wadanda su ka rasu, ya kasance ne a asibiti da kuma cibiyoyin kiwon lafiya a yankin Darfur, saboda a can ne ake da cibiyoyin kiwon lafiya mafi tabarbarewa a duniya.
A cikin watan Ogusta kadai an sami kananan yara 30,000 wadanda suke fama da tamowa.
A jiya Talata ne dai kungiyar ta “Doctors Without Borders” ta fitar da rahoton tana mai kara da cewa, abinda yake faruwa sakamako ne na yakin da kasar ta tsunduma a cikinsa tun daga watan Aprilu na 2023.