Rahotanni daga Sudan na cewa sojoji sun kai hare-hare ta sama da manyan bindigogi a Khartoum babban birnin kasar yau Alhamis.
Yayin da rikicin kasar Sudan ya kasance daya daga cikin jigon tattaunawa a zauren Majalisar Dinkin Duniya tare da wani sabon kira na kawo karshen fadan, bayanai sun ce an gwabza kazamin fada da sanyin safiyar yau Alhamis a babban birnin kasar, Khartoum, tsakanin sojoji da dakarun rundinar kai daukin gaggawa ta RSF.
Da misalin karfe 2 na safiyar yau ne sojojin kasar Sudan suka kaddamar da farmakin a wasu wurare na dakarun (RSF) a babban birnin kasar, inda akayi ta musayar wuta da manyan bindigogi kamar yadda mazauna birnin suka shaidawa masu aiko da rahotanni.
A cewar wata majiyar soji, sojojin sun kwace wasu manyan gadoji guda biyu, wato gadar White Nile da kuma gadar McNimir, wadanda suka raba sassan da sojojin ke rike da su a babban birnin kasar da wadanda ke hannun dakarun.
Wannan dai shi ne babban farmaki na farko da sojojin suka kai cikin kusan watanni hudu a kokarin dawo da martabar birnin Khartoum, wanda har yanzu yawancinsa na karkashin ikon dakarun Janar Hemedti.
Wannan farmakin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rundunar sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan zai yi jawabi a yammacin yau a Majalisar Dinkin Duniya.