Tsarin shari’a na kasar Spain zai hada kai da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da kotun duniya domin binciken laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza.”
Wannan yunkurin “ya mayar da martani ga shawarar rahoton kwamitin bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya mai zaman kansa (IOC) kan yankin Falasɗinawa da aka mamaye, wanda ya bukaci bangarorin Amurka su ba da hadin kai ga binciken da ofishin mai shigar da kara na kotunan manyan laifuka ta kasa da kasa.”
Za a sanar da sakamakon binciken ga kotun kasa da kasa da kuma ofishin mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
ministan harkokin cikin gida na Spain, Fernando Grande-Marlaska, ya goyi bayan matakin shari’ar na Spain, yana ganin ya na da”ma’ana” da kuma ya zama “wajibi” don bincikin laifuffukan da aka aikata a Gaza ta fuskar “kisan kare dangi”.
Kasar Spain ta nuna goyon bayanta ga al’ummar Palastinu, inda aka gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Madrid da wasu garuruwa domin yin tir da yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza.
Har ila yau kasar na cikin wadanda suka shiga shari’ar da Afirka ta Kudu ta fara a gaban kotun kasa da kasa, tana zargin Isra’ila da aikata kisan kiyashi a zirin Gaza.