Sojojin Yemen Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Babban Filin Jirgin Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Rundunar sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami Rundunar sojin Yemen ta sanar da kaddamar da farmakin

Rundunar sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami

Rundunar sojin Yemen ta sanar da kaddamar da farmakin soji kan babban filin tashin jiragen saman Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma yin nuna kiyayya ga kisan kiyashin da makiya ‘yan  sahayoniyya suke yi wa ‘yan uwansu a Zirin Gaza.

Kakakin rundunar sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya bayyana cewa: Don goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmaya da kuma nuna rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya ‘yan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a yankin Zirin Gaza, sojojin Yemen suna ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzami kan babban filin jirgin sama na Lod, wanda haramtacciyar kasar Isr’ila ke kira da filin jirgin saman Ben Gurion, a yankin Jaffa da suka mamaye.

Janar Yahya Sari’e ya kara da cewa: Suna kai hare-haren da makamai masu linzami masu linzami, domin tarwatsa yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments