Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Jiragen Ruwan Kasar Birtaniya A Tekun Bahar Maliya

Sojojin ruwan Birtaniya sun sanar da cewa: Jiragen ruwan Birtaniya guda biyu sun kama da wuta a gabar tekun Yemen Kamfanin dillancin labaran reuters ya

Sojojin ruwan Birtaniya sun sanar da cewa: Jiragen ruwan Birtaniya guda biyu sun kama da wuta a gabar tekun Yemen

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wasu hukumomin ruwa na kasar Birtaniya guda biyu a jiya Lahadi suna cewa: Sun tabbatar da cewa jiragen ruwan Birtaniya guda biyu sun kama da wuta bayan da sojojin Yemen suka kai musu hare-hare da makamai masu linzami a gabar tekun Aden dake kudancin kasar Yemen.

Hukumar tsaron ruwa ta Birtaniya “AMBREI” ta fitar da sanarwa cewa: An samu nasarar kashe gobarar da ta kama a jirgin ruwan dakon kaya da mayakan Yemen suka kai masa hari da makami mai linzami daga nisan kilomita 83 a shiyar kudancin birnin Aden na kasar Yemen.

A nata bangaren kuma, Hukumar Kasuwancin Maritime ta Burtaniya (UKMTO) da Rundunar Sojin Ruwa ta Biritaniya ke tafiyar da ita, ita ma ta bayar da rahoton afkuwar lamarin a nisan mil 70 kudu maso yammacin Aden na kasar Yemen.

Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin Yemen suke ci gaba da gudanar da ayyukansu a cikin tekun Bahar Maliya kan jiragen ruwan haramtacciyar kasar Isra’ila ko kuma wadanda ke kan hanyar zuwa haramtacciyar kasar ta Isra’ila, a matsayin taimakawa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma mayar da martani ga Amurka da Birtaniya kan ta’addancin da suke aiwatarwa kan kasar Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments