Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Yankin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin

Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami

Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa da makiya yahudawan sahyoniya suka aikata a kan ‘yan’uwansu a zirin Gaza, da kuma mayar da martani kan gungun yahudawan sahayoniyya da suke kutsawa cikin masallacin Al-Aqsa tare da wulakanta farfajiyar sa mai alfarma.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa; Rundunar ta kai wani harin soji mai inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Palestine 2.

Sanarwar ta bayyana cewa: Aikin ya samu nasarar cimma burin da aka sanya a gaba, godiya ga Allah, kuma ya sa miliyoyin gungun yahudawan sahayoniyya suka tsere zuwa maboyar karkashin kasa lamarin da ya kawo tsaiko ga ayyukan tashar jirgin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted