Sojojin kasar Yemen sun kai hare-hare kan yankin masana’antar gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila
Rundunar Sojin Yemen ta sanar da cewa: Sojojin saman kasarta sun kai wasu hare-haren soji masu inganci da jiragen sama marasa matuki ciki kan yankin masana’antu na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Asqalan da ke kudancin Falasdinu da aka mamaye.
Kakakin rundunar sojojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin cewa: Sojojin Yemen sun kai hare-haren ne da jiragen sama marasa matuka ciki, kuma sun yi nasarar kai wa yadda aka saita su, yana mai bayyana cewa: Aikin ya zo ne a cikin tsari na mataki na biyar na kara zafafa mayar da martani ga laifukan da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza da Lebanon.
Har ila yau, sojojin Yemen sun sake tabbatar da cewa: Ba za su dakatar da ayyukan soji kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba, matukar sojojin yahudawan sahayoniyya ba su daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa da kasar Lebanon ba.