Sojojin Isra’ila sun kai hari kan masu gadin kayan agaji a Gaza tare da aiwatar da wani mummunan kisan kiyashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wasu munanan hare-haren wuce gona da iri kan wuraren ajiye kayayyakin jin kai a biranen Rafah, Khan Yunus da suke kudancin yankin Zirin Gaza a daren jiya Laraba wayewar garin garin yau Alhamis, inda suka yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa masu yawa tare da jikkata wani adadi, sannan sojojin suka yi kuguden wuta ta hanyar jiragen saman yaki kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Zirin Gaza.
Majiyoyin yada labarai sun rawaito cewa: Falasdinawa 7 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani luguden wuta ta hanyar jiragen saman yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a kan jami’an ba da agajin jin kai kusa da yankin Al-Akawakh da ke kan titin Al-Rashid a shiyar yammacin birnin Rafah.
An kuma bayyana cewa, sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hari kan wata kungiyar da za ta kai agaji a mashigin Al-Nus da ke yammacin yankin Mawasi na birnin Khan Yunus, lamarin da ya kai ga shahada da jikkata mutane.