Sojojin ‘Yan Sahayoniyya Sun Sake Kai Wani Mummunan Hari Kan Kasar Lebanon

Mutane 72 ne suka yi, yayin da wasu 392 suka samu raunuka sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan kasar Lebanon a

Mutane 72 ne suka yi, yayin da wasu 392 suka samu raunuka sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan kasar Lebanon a jiya Laraba

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Adadin mutanen da suka yi shahada a hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a jiya Laraba ya kai shahidai 72 da suka hada da mata da kananan yara, sannan sama da 392 suka samu raunuka.

Jami’in kula da shirin gaggawa na gwamnatin Lebanon kuma ministan kula da yanayi Nasir Yasin ya sanar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada a kasar Lebanon tun daga ranar 8 ga watan Oktoban shekara ta 2023 zuwa yanzu sun kai mutane 1,247, yayin da wadanda suka jikkata suka haura zuwa 5,278, kuma yawancinsu fararen hula ne da suka hada da yara da mata.

Yasin ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasa matsugunnansu kuma suka samu mafaka a cibiyoyin tsugunar da ‘yan gudun hijira sun kai mutane 52,900, wadanda aka raba tsakanin cibiyoyi 360, kuma akasarinsu cibiyoyin ilimi ne da makarantun gwamnati.

Ministan ya kara da cewa: Wadannan mutanen da suka rasa matsugunansu suna wakiltar kusan kashi 30 cikin 100 na daukacin al’ummar kasar da suka rasa matsugunansu daga yankunansu sakamakon hare-haren kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments