Sojojin Yahudawan Sahayoniyya Sun Kashe Falasdinawa 121 A Yau Talata  

Hare-haren wuce gona da irin sojojin yahudawan sahayoniyya kan Gaza sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa 121 tun wayewar garin yau Talata Majiyoyin lafiyar Falasdinu sun

Hare-haren wuce gona da irin sojojin yahudawan sahayoniyya kan Gaza sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa 121 tun wayewar garin yau Talata

Majiyoyin lafiyar Falasdinu sun bayyana cewa: Hare-haren sojojin yahudawan sahayoniyya sun kai munanan hare-hare kan yankunan Falasdinawa da suke Zirin Gaza, inda suka janyo shahadan Falasdinawa 121 tun daga wayewar garin yau Talata, kuma 110 daga cikinsu a shiyar arewacin Gaza ne.

Tun da farko dai ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kashe Falasdinawa 4 iyalan gida guda a Zirin Gaza, sannan aka kai wasu gawawwakin shahidai 41 da wasu 113 da suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka yi shahada a hare-haren sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila kan yankunan Falasdinawa sun kai shahidai 43,061 da kuma wadanda suka jikkata da yawansu ya kai 101,223 tun daga ranar bakwai ga watan Oktoban bara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments