Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza.
Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI.
Amma sojojin sun kammala da cewa a halin yanzu yakin yana cinye rayuwar fursononin da hamas take tsare da su a gaza ne da kuma sojojin da suke fafatawa da su.