Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa unguwar Al-Zeitoun tare da lalata gidajen Falasdinawa kusan 400 Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana cewa: Kwanaki shida

Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa unguwar Al-Zeitoun tare da lalata gidajen Falasdinawa kusan 400

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana cewa: Kwanaki shida ke nan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ke luguden wuta a unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza, inda suka lalata gidaje kusan 400, ta hanyar jefa musu bama-bamai tare da yi musu luguden wuta da jiragen yaki.

Hukumar kula da kare hakkin bil adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Safa ya samu a yau Asabar cewa: Wannan na zuwa ne a wani bangare na farmakin da sojojin mamaya suka kai da nufin rusa yankin zirin Gaza, kwatankwacin abin da ya faru a yankunan Rafah, Khan Yunis, da kuma arewacin zirin Gaza. Manufar ita ce koran mazauna su tare da tilasta musu gudun hijira, a matsayin wani bangare na kisan kiyashin da take yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.

Masu Sanya ido kan al’amuran sun kara da cewa: Farmakin da sojojin na Isra’ila suka kai a unguwar Zeitoun, wanda aka fara tun ranar 11 ga watan Agusta, wani shiri ne da gwamnatin mamayar Isra’ila ta ayyana na shimfida cikakken ikonta ba bisa ka’ida ba a kan birnin Gaza da kuma tilastawa mazaunanta gudun hijira zuwa arewacin zirin Gaza – wanda aka kiyasta yawansu ya kai kimanin miliyan daya – zuwa wuraren da ba’a rayuwa a wajen da yake kan iyaka da yankunan kudancin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments