Sojojin mamayar Isra’ila da suka sake yin Kutse cikin yankunan kasar Siriya sun gudanar da sintiri a yankunan tare da kafa shingen binciken ababan hawa tsakanin Khan Arnabeh da kauyen Jaba da ke lardin Quneitra. Sintirin ya kunshi yahudawan sahayoniyya goma masu magana da harshen Larabci na ka’ida kuma suna sintirin ne a motoci kirar Hummer.
A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya, sojojin mamayar Isra’ila biyu kuma sun kutsa kai a tsakanin garuruwan Jaba da Khan Arnabeh, kusa da tsohon wurin binciken ababan hawa na Al-Saqri. Sun samu rakiyar motocin sojoji dauke masu rakiya kusan 20.
Sojojin suna gudanar da binciken motocin ne domin neman makaman da ke iya zama barazana ga tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila, lamarin da ya janyo cece-ku-ce tsakanin jama’a da bullar fargabar cewa: Wannan mummunan ci zarafi kan kasar Siriya zai iya ci gaba da janyo tada zaune tsaye.