Rahotonni sun bayyana cewa: A rana ta biyu a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar zirin Gaza da ke fama da yunwa.
Shafin yanar gizo na Falestine Today ya watsa rahoton cewa: A safiyar yau Litinin 2 ga watan Yunin shekara ta 2025, sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da wani sabon laifi ta hanyar kai hare-hare kan Falasdinawa a kusa da cibiyar bada agajin Amurka da ke birnin Rafah. Ya zuwa yanzu dai wannan aika-aika ya yi sanadin shahadan Falasdinawa 3 tare da raunata wasu 60, ba a ma maganar laifin da aka aikata jiya a gaban duniya, inda aka zubar da jinin al’umma sama da 30 da kuma jikkata wasu daruruwa na daban a wurin karbar agajin abinci.
Majiyoyin cikin gida sun tabbatar da cewa: An kai wa daruruwan Falasdinawa hare-hare ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa cibiyar ba da agaji da ke Rafah, inda hare-haren suka yi sanadaiyyar shahadar Falasdinawa 3, sannan wasu fiye da 60 suka jikkata.