Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis
A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da matsugunan ‘yan gudun hijira da suke Gaza, a matsayin matakin farko na hare-harensu a yau Litinin.
Bayan nan Sojojin mamayar sun farma garin Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza, inda suka kai wasu munanan hare-hare kan garin da jiragen saman yaki da suka aiwatar da mummunan kisan kiyashi a makarantar Fatima Bint Asad, da ya zama mafaka ga ‘yan gudun hijira.
Hare-haren bama-bamai biyu da aka kai kan makarantar ya yi sanadiyar shahadan fararen hula 16 tare da jikkata wasu, bayan da daya daga cikin jiragen ya kai hari a ajujuwa biyu har sau biyu a jere.
Haka a Jabaliya matashin bafalasdine mai suna Adham Al-Amital ya yi shahada sakamakon harin bam da jirgin sojin Isra’ila ya kai kan yankin “Abd Rabbo” da ke gabashin sansanin.