Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza.
Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma har yanzu ba a san ko su waye ba.
Wannan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, wanda ke nuni da irin mummunan halin jin kai da fararen hula ke fuskanta a zirin Gaza.