Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun yi luguden wuta da makami mai linzami kirar Zulfiqar kan birnin Yaffa na haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin kasar Yamen sun kai farmakin

Sojojin Yemen sun yi luguden wuta da makami mai linzami kirar Zulfiqar kan birnin Yaffa na haramtacciyar kasar Isra’ila

Sojojin kasar Yamen sun kai farmakin soji guda biyu a kan yankunan Yaffa da Umm al-Rashrash na haramtacciyar kasar Isra’ila, a cikin tsarin kashi na biyar na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan mamaya, domin nuna goyon baya ga gwagwarmayar Falastinawa da na Lebanon, kuma hare-haren sun zo ne a dai dai lokacin da ake tunawa da harin daukan fansa da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka kai harin “Guguwar Al-Aqsa”.

Rundunar sojin kasar ta Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Harin farko an kai shi ne kan wasu wurare biyu na sojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin “Yaffa” da aka mamaye da makamai masu linzami guda biyu, kirar “Falasdinu 2”, wanda ya yi nasarar isa daidai inda aka harba shi, sai kuma na biyu da makamin “Zulfiqar”.

Har ila yau, Sojojin na Yemen sun harba jiragen saman yaki marasa matuka ciki kan wurare da dama a yankin “Yaffa” da kuma yankin “Umm al-Rashrash” da ke kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye, ta hanyar amfani da jirage nau’in “Yaffa” da “Sammad 4”, wanda ke nuni da cewa da yawa daga cikin wadanan jiragen sun yi nasarar kai wa ga wuraren da aka tsaita su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments