Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa, adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 2792 daga cikinsu da akwai kananan yara 160, wadanda su ka jikkata kuma sun kai12,772.
Bugu da kari ma’aikatar harkokin kiwon lafiyar ta Lebanon ta ce a ranar Litinin kadai, an sami shahidai da su kai 82, wadanda su ka jikkata kuwa sun 180.
A garin Sarfand hrin na jiragen yakin HKI sun yi sanadiyyar shahadar mutane 8 da jikkata wasu 21.
A garin Saida ma sojojin mamayar sun kashe mutane 6 tare da jikkata wasu 37.
Kashe fararen hula da HKI take yi, yana zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan gwagwarmaya suke kashe sojojinta a fagen daga.