Sojojin HKI Sun Yi Furuci Da Rashin Nasarar Samun Nasarar Jagoran ‘Yan Gwagwarmayar A Beit Hanun

Bayan kusan shekara daya da HKI ta sanar da cewa ta kashe kwamandan ‘yan gwgawarmaya na yankin Beit-Hanun, Husain Fayyad          ( Abu Hamza) sai dai

Bayan kusan shekara daya da HKI ta sanar da cewa ta kashe kwamandan ‘yan gwgawarmaya na yankin Beit-Hanun, Husain Fayyad          ( Abu Hamza) sai dai kuma a jiya Laraba ya fito a tsakiyar mutane yana jawabi.

Wani faifen bidiyon da aka watsa a jiya Laraba ya nuna Husain Fayyad yana Magana a tsakanin ‘yan gwgawarmaya da kuma nasarar da aka samu a Gaza.

A cikin watan Mayu na shekarar da ta gabata 2024 ne dai  kakakin sojojin HKI  ya sanar da cewa; sun kashe Abu Hamza a wani fada da su ka yi a wani ramin karkashin kasa.

Kafafen watsa labarun HKi sun ce bayan watanni shida da sojojin Isra’ila su ka sanar da kashe shi, Abu Hamza ya bayyana yana Magana da mutanen Gaza, sannan kuma yana kalubalantar Isra’ila.

Wani malamin tarihin HKI Our Filakov ya ce, Abinda ya faru da akwai i kunya a ce Husain Fayyad da sojoji su ka ce sun kashe ashe yana nan a raye.

A jiya Laraba kakakin sojojin HKI ya bayana bayyanar Fayyad da cewa abin kunya ne.

A gefe daya ministan yakin HKI, ya sanar da cewa suna da shirin aitawar da salon yakin Gaza a yammacin kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments