Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza
Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu,
Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama.
Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata tare da kona gawarwakinsu sakamakon yin luguden makamai masu linzami kan sansanoninsu musamman wadanda suke rayuwa a cikin tantuna a yankin al-Mawasi da ke yammacin Khan Yunis.