Shugabannin kungiyoyin raya kasashen gabashi da kuma kusanci na Afrika (EAC da SADC), sun yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a gabashin Jamhuriyar DR Congo.
Bangarorin sun bayyana hakan a wani taron hadin guiwa da suka gudanar a birnin Dar es Salaam, na kasar Tanzania a jiya Asabar.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun kuma bukaci da bude manyan tituna da filin jirgin saman Goma, da kuma tattaunawa kai tsaye tsakanin Kinshasa da kungiyar M23.
Saidai taron, bai yi Allah wadai da Rwanda ba kan shigar ta cikin rikicin ba.
Taron na hadin gwiwa ya tabbatar da hadin kai da jajircewa wajen ci gaba da marawa DRC baya a kokarin da take yi na kare ‘yancin kanta, da ikonta da kuma yankunanta,” a cewar sanarwar karshen taron.
A nata bangaren, tawagar ta Rwanda ta yi imanin cewa, wannan taro ya cika burin Kigali.
Wanda ya bada dama don dawo da zaman lafiya a gabashin DRC”, a cewar ministan harkokin wajen kasar a shafinsa na X.
“Taron na hadin gwiwa ya bukaci shugabannin rundunar tsaro ta AEC (Al’ummar Gabashin Afirka) da SADC (Al’ummar Gabashin Afirka ta Kudu) da su gana cikin kwanaki biyar don fidda hanyoyin tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba da kuma dakatar da fada.