Shugaban Senegal Ya Ce: Kafa Sansanin Sojin ‘Yan Mulkin Mallaka A Kasa Ya Sabawa ‘Yancin Kan Kasar

Shugaban kasar Senegal ya bayyana cewa: Senegal kasa ce mai cin gashin kanta don haka bai dace a ce akwai sansanonin sojan Faransa a cikinta

Shugaban kasar Senegal ya bayyana cewa: Senegal kasa ce mai cin gashin kanta don haka bai dace a ce akwai sansanonin sojan Faransa a cikinta ba

Shugaban kasar Senegal Basirou Diomai Faye ya bayyana a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewa: Za su tilastawa Faransa rufe sansanonin sojinta da ke Senegal, saboda kasancewar sansanonin ya ci karo da ‘yancin kan kasar ta Senegal.

Shugaban ya kara da cewa: Senegal kasa ce mai cin gashin kanta, don haka ‘yancin kai bai dace da kasancewar sansanonin ‘yan mulkin mallaka a kasar ba.

Faye, wanda ya hau kan karagar mulki a watan Afrilun wannan shekara bayan ya lashe zabe, ya daga tutar ‘yancin kai na kasar Senegal da kuma kawo karshen dogaro da kasashen waje, yana mai jaddada cewa kin amincewa da sojojin Faransa a kasarsa, ba yana nufin raba gari ne tsakanin Senegal da Faransa ba.

Kanun labarai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments