Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu.

Kalaman shugaban na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa ‘yan bindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna “yi wa Kiristoci kisan gilla”

Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a jiya Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen”ta’addanci”.

“Duk da kalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da kawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance,”

“Ina tabbatar muku cewa za mu kawo karshen ta’addanci. Abin da muka saka a gaba shi ne cigaba da ayyuka ido bude bisa manufarmu ta Sabunta Fata [Renewed Hope] domin gina Najeriya mai yalwa.”

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted