Shugaban Mulkin Sojin Gambiya Ya Yi Wa Kansa Karin Girma Zuwa Cikakken Janar

Shugaban mulkin sojin kasar Guinea Kanal Mamadi Doumbouya ya yi wa kansa karin girma zuwa mukamin cikakken Janar. Doumbouya, mai shekaru 43, ya kwace mulki

Shugaban mulkin sojin kasar Guinea Kanal Mamadi Doumbouya ya yi wa kansa karin girma zuwa mukamin cikakken Janar.

Doumbouya, mai shekaru 43, ya kwace mulki ne da karfin soji a watan Satumbar 2021 ta hanyar hambarar da shugaba Alpha Conde.

A wata doka da aka karanto a yammacin ranar Juma’a, Doumbouya, wanda magoya bayansa suka bukaci ya tsaya takarar shugaban kasa a lokacin da sojojin kasar ke son mika ragamar mulki ga farar hula an ba shi lambar yabo mafi girma a kasar.

An ba shi lambar yabo ne sakamakon yunkurinsa na kara hada kan jama’ar kasar.

karin girman da Janar Doumbouya ya yi wa kansa na zuwa ne kwanaki bayan takwaransa na Mali Assimi Goita shi ma ya yi wa kansa karin girma daga mukamin kanal zuwa cikakken janar.

Doumbouya na daya daga cikin jami’an soji da dama da suka kwace mulki a yammacin Afirka tun daga shekarar 2020, tare da wasu shugabannin sojoji a Mali, Burkina Faso da Nijar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments