Shugaban Majalisar Shawarar Ta Iran Ya Aika Sako Ga Takwarorinsa Na Duniya

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya aike da sako ga Majalisun Dokokin Kasashen duniya yana jaddada rawarsu a fagen dakatar da zalunci kan al’ummar

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya aike da sako ga Majalisun Dokokin Kasashen duniya yana jaddada rawarsu a fagen dakatar da zalunci kan al’ummar Falasdinu

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga shugabannin majalisar dokokin duniya da su bayyana matsaya ta bai daya a gaban tarukan kasa da kasa domin gurfanar da yahudawan sahayoniyya kan laifuffukan da suka aikata a gaban kuliya da kuma hana ta aiwatar da kisan kiyashi.

Qalibaf ya jaddada cewa: Bisa la’akari da yanayin da ake ciki, inda yahudawan sahayoniyya suke aiwatar da sabbin ayyukan kisan kiyashi a idon duniya, kuma a daidai lokacin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ta gaza kawo karshen yakin Gaza. da kuma wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suke yi kan Falastinu da Lebanon, wajibi ne a dauki kwararan matakai daga kasashen duniya da nufin dakatar da hare-haren soji kan wadannan kasashe da kuma samar da hanyar fita daga cikin mawuyacin halin da ake ciki a halin yanzu da ya zama wata lalura da ba za a yi watsi da ita ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments