Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki.
Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da dama suka watsa kai tsaye.
Sheikh Qasim yace kasar Lebanon za ta ci gaba da zama kasa mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka HKI ta mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar.
Shugaban kungiyar ya jaddada bukatar sake gina wuraren da HKI ta rusa a yankunan daban daban na kasar, ya ce gwamnatin kasar ta yi alkawalin za ta sake gina wuraren da HKI ta rusa a yakinta da hizbullah na baya-bayan nan.
Sheikh Qasim ya ce rashin yin haka, nuna bambanci ne a tsakanin mutanen kasar. Ya ce dangane da wadanda aka rusa gidajensu kungiyar ta bada kudaden haya ga mutane 50,755 , sannan ta gyara wasu 332 da aka lalata, wanda duk aikin gwamnati ne, yin hakan. Don haka akwai bukatar gwamnati ta aikata wajibin da ya hau kanta.